
Babban bankin Najeriya (CBN) Ya musanta wata sanar wa da ta fita kan cewa darajar Naira ta karye a hukumance.


Hakan ya fito ne ta bakin Mukaddashin Daraktan bankin Abdulmuminu,
Abdulmuminu, yace ko a jiya Laraba an siyar da dala ɗaya a kan naira 465.
Ya kuma kara da cewa Rahoton da ya fita kan sanarwar karyewar darajar Naira ba gaskiya ba ne.
Bankin ya shawarci Mutane da su yi watsi da Rahoton da su ka ji kan karyewar darajar Nairar.