Wani rikici ya barke a tsakanin masu ababan Hawa a Jihar Ondo bayan janye tallafin Man fetur da gwamnatin tarayya ta yi a fadin Kasar.

Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis a Akure babban birnin Jihar.

Rikicin ya barke ne tsakanin masu adaidaita sahu da masu mota tasi saboda farashin sufuri bayan tashin farashin Man ferur.

Direbobin motar tasi sun zargi masu adaidaita sahu da daukar fasinjoji a kudi mai sauki sabanin yadda su suke dauka saboda karin farashin man.

Rahotanni sun bayyana cewa direbobin tasi sun kara kudin motar tafiya daga Jami’ar Fasaha ta Tarayya FUTA zuwa kasuwar Ojaoba daga N200 zuwa N300, amma masu adaidaita sahu suna daukar fasinja akan naira 200 kacal.

Direbobin motar tasin sun yi wani zama da dukkan ‘yan uwansu masu motar don hana masu adaidaita sahun daukar fasinja a wannan farashi.

Mafi yawan fasinjojin sun koma hawa babur na ‘yan acaba don samun sauki yayin da ake ta rikici tsakanin direbobin tasi da adaidaita sahu akan karin farashin.

Wani direba mai suna Mista Olawale Ajayi ya ce ba fada suke da masu adaidaita sahu ba kawai suna bukatar amincewarsu ne akan karin farashin kudin.

Direbobin motar sun bayyana cewa ba za su samu kudi ba idan suka cigaba da daukarsu a tsohon farashi suke wanda hakan ka iya cutar dasu.

Wani direba ya kara da cewa ba za su iya kai balas ba Naura 4,000 ba idan suka sayi lita 30 akan kudi N15,000.

Leave a Reply

%d bloggers like this: