Gwamnatin Jihar Kano ta fara gudanar da aikin rushe wasu gine-gine da aka yi a filayen gwamnatin Jihar.

Babban sakataren yada labaran gwamnan Jihar Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya tabbatar da hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.

ya ce gwamnan Jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ne bayar da zinin fara rushe gine-ginen wadanda ya ce an yi su ba bisa ka’ida ba a wasu gurare wanda ya kasance mallakin gwamnatin Jihar.

Sanarwar na bayyana cewa an fara aikin rushe guraren ne a safiyar ranar Asabar, inda aka fara da wasu gine-gine da ke filin Sukuwa a Kano domin Kwato filin da ya kasance mallakin gwamnatin Kano.

Gwamnan ya ce za a rusa guraren da aka gina a filayen makarantu da Masallatai da Filayen Wasanni da Maƙabartu da Kasuwanni da kuma Asibitoci domin tabbatar da bin tsare-tsare a Kano
tare da Kawata ta da kuma tsare lafiya da dukiyoyin al’ummar Jihar.

Sanarwar ta bukaci mazauna Kano da su yi hakuri kasancewar sabuwar gwamnatin Jihar na son tabbatar da ci gaban Jihar.

A yayin jawabin ratsuwar kama aiki da gwamnan yayi ya bai’wa jami’an tsaro izinin kwato kadarorin gwamnatin Jihar da ya ce tsohuwar gwamnatin Ganduje ta sayar ga wasu mutane a Jihar.

Sanarwar ta ce a ranar Juma’a gwamnan ya bayar da umarni ga masu gine-gine a filin da ke bayan sansanin alhazai na Hajj Camp a Jihar da su gaggauta dakatar da ginin bayan wata ziyara da ya kai wajen.

Leave a Reply

%d bloggers like this: