Shugaban Najeriya Asiwaju Bola Ahmad Tinubu ya aike da sakon jajantawa ga gwamnatin Kasar Indiya sakamakon hadarin Jiragen Kasa wanda ya hallaka fiye da mutane 250 a Kasar.

 

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban Kasa Tinubu kan yada labarai Abdulaziz Abdulaziz ya fitar.

 

Shugaban na Najeriya ya kuma mika sakon jaje ga iyalan wadanda hadarin jirgin na Kasa ya rutsa da su a Jihar Odisha ta Kasar.

 

Bola Tinubu ya sake mika sakon ta’aziyyar sa ga firaministan Kasar Narendra Modi da Al’ummar Kasar ta Indiya tare da iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su.

 

Hadarin ya rutsa da Jiragen Kasa guda biyu cike da fasinjoji da kayayyaki a birnin Baladsore a jihar Odisha da ke gabashin ƙasar.

 

Sama da mutane 900 ne suka samu raunuka a hadarin.

 

Hadarin da ya afku ya kasance daya daga cikin hadari mafiya muni a tarihin ƙasar.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: