Gwamnatin kasar Indiya ta bayar da umarnin ci gaba da zirga-zirga a titin jirgin ƙasan da aka yi hatsari a makon jiya.

 

Jirage uku ne su ka yi hatsari a layin dogon a ranar Juma’a wanda hakan yay i sanadiyyar mutuwar mutane sama da 200.

 

Lamarin ya faru a Odisha samakamakon taho mu gama da jiragen uku su ka yi wanda hakan ya haifar da mummunan hatsarin da yay i silar rasa rayuwar mutane kusan 300.

 

Rahotanni sun ce hatsarin yay i silar jikkata mutane sama d 1,000 kuma tuni aka kais u asibiti domin kula da lafiyarsu.

 

Mahukunta a kasar sun fara bincike domin gano dalilin faruwar hatsarin.

 

Sai dai har yanzu bas u bayyana dalilin da ya sa lamarin ya faru ba.

 

Shugabanni na ta aike da saƙon jaje ga gwamnati da iyalan waɗanda lamarin ya rutsa da su, kamar yadda shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aike da sakon a ranar Asabar.

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: