Aƙalla mutane sama da 60 ne su ka rasa rayuwrasu yayin da ƴan bindiga su ka kai hari wasu ƙauyuka a jihohin Sokoto da Zamfara.

Ƴan bindiga sun kai hari Raka, da Raka Dutse da kuma garin Filingawa a ƙaramar hukumar Tangaza a jihar Sokoto sannan su ka kashe mutyane 37.


Lamarin ya faru a makon da ya gabata kasa da mako guda bayan da sabbin shugabanni su ka fara aiki a Najeriya.
Wani shaidar gani da ido y ace an kai harin a ranar Asabar da yamma kuma an hallaka mutane 18 a garin Raka, sannan an kashe mutane 17 a garin Filingawa da Raka Dutse.
Ya ce mazauna ƙauyukan wasu sun samu raunin harbin bindiga a jikiinsu, yayin da wasu da dam aba a gansu ba.
Ko a jihar Zamfara ma sai da ƴan bindiga su ka kai hari tare da kashe mutane a ƙananan hukumomin Maradun da Maru.
A garin Kanoma da ke ƙaramar hukumar Maru an kashe mutane 25 ciki har da ƴan ƙungiyar sa kai 16.
Haka ma a garin Janbako ƴan bindigan sun hallaka sama da mutane 20 a Asabar ɗin makon jiya.
Sannan sun kashe wasu mutane biyar a ƙauyen Sakkida.
Sai dai jami’an ƴan sanda a jihar bas u magantu a kan lamarin ba.
Babban mataimaki ga gwamnan jihar a kan kfafen watsa labarai a jihar Zamfara Mustapha Jafaru Kaura y ace lamarin ya faru ne a lokacin da gwamnan ke kokari wajen ganin an kawo ƙarshen ƴan bindiga tare da tsare rayuwa, lafiya da dukiyoyin al’umma.
