Aƙalla mutane takwas aka hallaka a wani sabon hari da aka kai garin Rawuru a jihaar Filato.

 

Garin Rawuru na karkashin karamar hukumar Barikin Ladi a jihar.

 

Harin an kai a daren Juma’a wayewar ranar Asabar, wanda ya yi silar salwantar da rayuwar mutane Takwas.

 

Wani shugaban matasa a ynakin ya ce ko a ranar Litinin makon jiya.

 

Solomon Daylop ya bayyana mamakinsa dangane da yadda aka ki kai daukin gaggawa a lokacin da mutanen ke cikin bukatar taimako.

 

Shugaban matasan yankin ya ce a wata guda an hallaka mutane 276 sannna mutane sama da 30,000 ne su ka rabu da muhallinsu.

 

Sai dai ya jinjinawa hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa Nema da hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar a kna kokarin taimakawa mabukatan da su ke neman dauki.

 

 

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: