Wasu da ake zargi ‘yan bindiga ne sun yi garkuwa da wani basarake mai suna Oba na Idofin da matarsa a hanyar Makutu-Idofin dake ƙaramar hukumar Yagba East a jihar Kogi.

Shugaban ƙaramar hukumar Yagba ta Gabas Mista Abdulrazak Asiru ya tabbatar da faruwar lamarin.

Suma wasu Shaidun gani da ido sun shaidawa jaridar Daily Trust cewa ‘yan bindiga sun yi garkuwa da barasaken ne da misalin ƙarfe 5:30 na yammacin ranar Litinin.

Shaidun sun bayyana cewa ‘yan bindigan sun tare kan hanyar ne ɗauke da makamai, inda suka yi awon gaba da basaraken da matarsa zuwa cikin daji.

Shugaban karamar hukumar ya ce sun shiga cikin tashin hankali bayan garkuwa da basaraken.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda Jihar SP William Aya ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kakakin ya ce bayan garkuwa da basaraken da matarsa su ka aike da jami’ansu da mafarauta cikin dajin don kubutar da su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: