A wani labarin kuma wasu mahara sun kone mutane 11 a jihar Filato.

Lamarin ya faru a daren ranar Talata a karamar hukumar Mangu ta jihar.
Wani da lamarin ya faru a kan idonsa ya ce yan bindigan sun shiga garin da misalin ƙarfe 11 na dare kuma da shigarsu su ka fara harbin mutane.


Wasu rahotanni sun ce an kone wata coci a daren kamae yadda wani Micheale Bulus ya shaida.
Da farko yan bindigan sun fara harbin kna mia uwa da wabi, daga bisani kuma su ka kone gawar mutane 11 kamar yadda su ka gani a safiyar yau Talata.
Duk da cewar jami’an yan sanda ba su magantu a kna lamarin ba, sai dai an ga an aike da jami’an da dama yankin domin tabbatar da tsaro.
