Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa tsohon gwamna Kano Rabiu Musa Kwankwaso ne ke mulkin Jihar.

Abba Kabir ya bayyana hakan ne a yayin rantsar da sabbin kwamishinoni a gidan gwamnatin Jihar a ranar Litinin.

Gwamnan ya ce kwarewa da gogewar Kwankwaso a matsayin wanda ya riƙe matsayin gwamna, kuma Sanata, da kuma Minista ya sanya ya zabe shi a matsayin jogoran da za a yi wa biyayya.

Abba ya kara da cewa kwarewar kwankwaso ce ta sanya su amfana da gogewarsa tare kuma da yi masa ladabi.

Gwamnan ya ce gwamnatinsa ta dauki matakin dakatar da albashin wasu ma’aikata 10,800 wadanda tsohon gwamna na Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya dauka aiki a kasarshen mulkinsa.

Sannan ya ce ba za su ci gaba da biyansu albashi ba sai bayan an kammala bincike akansu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: