Gwamnan jihar Neja Muhammad Umar Bago ya bai’wa Alhazan Jihar kyautar kudade a ƙasar Saudiyya.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwar da hadimin gwamnan kan sadarwa Abdulberqy U Ebbo ne ya fitar a shafinsa na Twitter a ranar Asabar.

Gwamnan ya bai’wa Alhazan su 3710 kyautar Riyal 100 kowannen su a Kasar wanda a kudin Najeriya yawansu ya kai naira 25,000.

Bago ya kuma bai’wa ma’aikatan Tara na wucin gadi da ma’aikata 25 da masu sanya ido 25 da shugabannin ƙananan hukumomin aka ba su Riyal 200.

Gwamnan ya bai’wa Alhazan kyautar ne a lokacin da ya ziyarce su a Mina da ke Kasar ta Saudiyya.

Hadimin ya kara da cewa kyauyar ta fito ne daga aljihun gwamnan ba daga aljihun Jihar ta Neja ba.

Gwamna Bago ya bayyana cewa ya yi musu kyautar ne bisa yabawa da halin nagarta da zamtowa wakilai nagari da suka nuna a Kasar.

Bago ya tabbatarwa da Alhazan cewa gwamnatin Jihar na iya bakin Koƙarinta wajen inganta aikin Hajji daga shekara mai zuwa, inda za ta fara da gyaran sansanin Alhazai da gyara filin tashi da saukar jiragen sama na Jihar da ke a birnin Minna babban birnin Jihar.

Gwamnan ya kuma ƙara da cewa za a samawa Alhazan ababen hawa masu kyau a ƙasar.

Daga ƙarshe ya yi addu’ar Allah ya amsa ibadar da suka gabatar ya kuma ba Jihar Neja zaman lafiya da ci gaba mai dorewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: