halin yanzu daai tsohon shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bar mahaifarsa ta Daura a jihar Katsina, bayanin nan ya fito ne daga bakin Garba Shehu.

A jawabin da ya fitar a shafinsa na Twitter a yammacin Alhamis, Malam Garba Shehu ya ce tsohon shugaban Najeriyan ba ya garin Daura.
Da yake bayani, mai magana da yawun bakin Muhammadu Buhari bai yi bayanin inda ya koma ba, sai dai ya fadi abin da ya jawo hakan.

Bayan wata daya ya na zaune a cikin mutanensa, sai ga shi labari ya zo cewa ya tattara ya bar gonarsa da dabbobinsa da yake sha’awa.

Garba Shehu ya nuna dattijon bai samu yadda yake so a garin na Daura, duk da ya bar kan mulki, mutane su na yawan kai masa ziyara.
Hadimin ya ce mai gidansa ya sake tafiya zuwa wani wuri mai nisa domin ya yi rayuwa a nitse.
Buhari ya koka da cewa masu ziyara su na yi masa cin-cin-rindo dare da rana, abin da ba zai so ba a lokacin da yake kokarin samun hutu.
Idan ba a mantaba tun kafin ya bar fadar shugaban kasa na Aso Rock Villa a watan Mayun 2023, Buhari ya yi alkawarin cewa zai zauna na watanni a mahaifarsa, daga bisani ya tafi kasar Niger.