Majalisar dattawa ta ce za ta gudanar da bincike kan kwangilar aikin gas da aka ba kamfanin Acugas Limited a lokacin tsohon shugaba Muhammadu Buhari.

Abin da ya jawo maganar kuwa shi ne batun da Sanata Aniekan Bassey na jam’iyyar PDD ya kawo a ranar Alhamis.

Aniekan Bassey ya ce a shekarar 2017 ne kamfanin lantarki nan na NDPHC ya shiga da yarjejeniyar Dala miliyan 10 da Acugas Limited domin samar da gas.

Wadda ta sa hannu domin a ba kamfanin Calabar Generation Company Limited gas din ita ce Zainab Ahmed, a lokacin ta na Ministar kudi da tattalin arziki.

Sanatan na Akwa Ibom ya ce makudan biliyoyin da aka batar ya jawo abin magana, kuma ana zargin akwai nuku-nuku wajen yadda aka biya kwangilar.

A dalilin haka, rahoton ya ce ‘dan majalisa ya bukaci idan an kafa kwamitin harkar lantarki, a bankado gaskiyar abubuwan da su ka faru wajen wannan aiki.

Za a so majalisa ta gayyaci duk wani ko hukuma da ke da hannu a kwangilar domin a ji ta bakinsu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: