Wata kungiya mai suna Save Nigeria Movement SNM tayi kira ga shugaban Kasa Bola Tinubu da ya yi taka tsantsan da tsohon Gwamna Jihar Ebonyi Dave Umahi.

Shugaban Kungiyar Rabaren Solomon Semaka ne ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a birnin tarayya Abuja.

Kungiya ta kuma aikewa da wani jawabi ga Jaridar Legit, inda ta ce Sanata David Umahi ya na neman saka dan uwansa ya zama Minista a gwamnatin Bola Tinubu.

Shugaban kungiyar ya kuma bukaci da Bola Tinubu idan zai nada Ministoci ya nada bangare daban-daban domin samun zaman lafiya a yankin kudu maso gabas.

Kungiyar na zargi David Umahi da maida sha’anin mulkin Jihar ya zama tamkar gadon danginsu wanda hakan ka iya kawo cikas ga zaman lafiyar Jihar.

Kungiyar na zargin Umahi da kai sunan dan uwansa na jini kuma jigo a jam’iyyar APC a Jihar domin ya samu kujerar Minista a mulki Tinubu.

Shugaban kungiyar ya ce ganin jita -jita ta yi yawa ne ya sanya suka ankarar da mutane game da bayar da sunan Austine Umahi domin ya zama Minista.

Leave a Reply

%d bloggers like this: