Wata ƙungiya a Najeriya ta zargi gwamnatin Kano da haddasa kiyayya da gaba tsakanin talakawa da gwamnatin tarayya.

 

Ƙungiyar mai rajin samar da walwala a tsakanin talakawa da marasa galihu a Najeriya ta soki batun gwamnatin jihar Kano na sukar tsarin raba tallafin rage radadin cire tallafin man fetur a ƙasar naira biliyan 500.

 

Kungiyar mai suna Welfare Of Poor And Vulnerable Nigerians (AWPON) ta ce gwamnatin Kano ƙarƙashin gwamna Injiniya Abba Kabir Yusuf ba ta yi nazari a kan tsarin da gwamnatin tarayya ta yi wajen raba tallafin ba.

 

Gwamnan Kano ta bakin mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam ya bayyana yayin wata ganawa da wata kungiya a Kano ranar Alhamis cewa, akwai tsantsar nuna bambanci a cikin tsarin raba tallafin.

 

Kwamared Aminu Abdussalam a yayin taron ya ce, kudin da za a raba naira biliyna 500, jihar Legas kaɗai za ta karbi kaso 47 na tallafin yayin da shiyyar kudu maso kudu za su karbi kaso 17 sauraan jihohin kuwa a raba musu kason da yake kasa da 50 wanda shi ne mafi ƙarancin.

 

Sai dai a wani bayani da coodinetan ƙungiyar Mr Sambo Dogo ya ce bai kamata a ce jihar Kano ce ta fitar da wannan sanarwa ba.

 

Ƙungiyar ta zargi gwamnatin Kano da fitar da bayanin domin haddasa kiyayya da gaba tsakanin al’umma da gwamnatin tarayya.

 

Sannan ƙungiyar ta alakanta baatun da zance mara tushe tare da rashin tabbatarwa da kuma ƙarancin gogewar aiki wajen tabbatarwa.

 

Sanarwar ta ci gaba da cewa, ya kamata gwamnatin Kano ta mayar da hankali don fuskantar ayyukan cigaba a jihar, amma sai ta fake da cin fuskar gwamnatin tarayya ta hanyar sukar tsarin tallafin da za ta bayar don rage radadin cire tallafin man fetur.

 

Bayanin ƙungiyar ya cigaba da cewa yayin da su ka ga sanarwar wadda sakataren yaɗa labaran mataimakin gwamnan ya fitar, sun girgiza ganin yadda gwamnatin Kano ta ce an tafka kuskure da take hakkin doka tare da nuna tsagwaron rashin dacewa wajen raba tallafin naira biliyan 500.

 

Sanarwar gwamnatin Kano ta yi kira ga hukumomi da masu ruwa da tsaki har ma da majalisar dokoki ta ƙasa ta da ta yi duk mai yuwuwa wajen ganin an dauki matakin da ya dace a kai.

 

Kungiyar ta ce sam gwamnatin Kano ba ta fahimci tsarin ba kuma sun tabbata shugaba Bola Ahmed Tinubu ba zai yi abinda ya saɓa da doka ko kundin tsarin mulki ba.

 

Sannan ƙungiyar ta ce gwamnatin Kano ba ta fahimci yadda tsarin mulki yake ba, a don haka ta ke fata Allah ya kwaci jihar Kano daga shugabanci mara tsari.

 

Kuma za ta cigaba da addu’a don ganin Kano ta fita daga tsarin mulki mara fasali da alkibla.

Leave a Reply

%d bloggers like this: