Tsohon gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya soki gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf bisa sukar shirin bayar da Naira biliyan 500 na tallafin Shugaban Kasa Tinubu domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur a Kasar.

 

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da tsohon kwamishinan yada labaran tsohon gwamnan Muhammad Garba ya fitar a ranar Lahadi.

 

Ganduje ya ce Abba Kabir ya yi saurin kalubalantar shirin bayar da tallafin ,inda kuma ya bukace shi da ya yi koyi da gwamnan Jihar Imo.

 

Tsohon gwamnan ya kuma dora alhakin rashin ƙwarewa da rashin fahimtar wasu abubuwa a matsayin babban dalilin da ya sanya gwamnatin ta ke yin kwan gwaba kwan baya da katoɓara wajen fitar da kalamanta.

 

Sannan ganduje ya shawarci Abba da ya bi sha’anin mulkisa sannu a hankali.

 

A baya dai gwamnatin ta Kano ta yi ƙorafi kan rabon tallafin Naira biliyan 500 domin bai’wa ‘yan Jihar.

 

Gwamnatin ta Kano na ganin a gurin rabon tallafin an fifita wasu Jihohin akan wasu.

 

Bayan kalaman na gwamnatin ta Kano aka buƙace ta da jam’iyyar ta NNPP da su samar da ingantaccen shiri wanda zai rage raɗaɗin da mutanen Jihar su ke ciki ba su ringa neman makusa ba a shirin gwamnatin tarayya na rage raɗaɗin tallafin man fetur.

 

Amma a yayin kalaman gwamnatin ta Kano ta yi watsi da Rahoton cewa ta soki gwamnatin tarayya kan rabon tallafin Naira biliyan 500,inda ta ce ba a fahimci Kalaman da ta yi ba akan tsarin rabon tallafin domin ragewa ‘yan kasar radadin cire tallafin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: