Rundunar ‘yan sandan Jihar Kwara ta yi cikakken bayani dangane da tsawar da ake zargin ta hallaka wasu masu garkuwa da mutane a yankin Oro Ago da ke karamar hukumar Ifelodun ta Jihar.

 

Rundunar ta yi karin hasken ne a ranar Lahadi inda ta bayyana cewa tsawar ta yi ajalin wasu makiyaya biyu ne ba masu garkuwa da mutane ba.

 

A cikin wata sanarwa da Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan Juhar SP Ajayi Okasanmi ya fitar, ya ce bayan kammala binciken faifan bidiyon da rundunar ta yi ta ce wadanda ake zargin sun kone yaran Fulani ne su biyu wadanda su ka kasance masu shekaru 10 da kuma 12.

 

Rundunar ta ce mutanen makiyaya ne wadanda tsawar ta hallaka ba masu garkuwa da mutane ba ne kamar yadda aka bayyana a cikin faifan bidiyon faruwar lamarin.

 

Amma kakakin bai yi cikakken bayani ba akan yadda lamarin ya faru.

 

Idan za a iya tunawa a ranar Litinin din da ta gabata ne dai wasu mazauna yankin na Oro Ago su ka bayyana cewa wadanda tsawar ta yi ajalinsu mutane uku ne wadanda su ka fito daga cikin masu garkuwa da mutane takwas da suka addabi yankin.

 

 

 

 

Hukumar yaki da sha da fataucin Miyagun Kwayoyi ta Kasa NDLEA ta kama wata lauya da ta kware wajen hadawa da kuma safarar miyagun kwayoyi a Jihar Legas.

 

Hakan na kunshe ta cikin wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na hukumar Femi Babafemi ya fitar a ranar Lahadi a birnin tarayya Abuja.

 

Femi ya bayyana cewa wadda ake zargin mai suna Ebikpolade Helen mazauniyar yankin Lekki ce da ke Jihar ta Legas, ta kware ne wajen hade-haden miyagun kwayoyi daban-daban da suke sanya mutane maye.

 

Kakakin ya kara da cewa sun samu nasarar kama lauyar bayan samun bayanan sirri da suka yi akanta a Awka babban birnin Jihar Anambra.

 

Inda suka kwace kilogiram biyar na ganyen tabar wiwi da kuma kwalaban kayan maye 12.

 

Kazalika Femi ya kara da cewa hukumar ta sake kama wani matashi mai suna Abubakar Shu’aibu a ranar 13 ga watan Yuli a kan hanyar Mushin-Oshodi da ke Jihar Legas dauke da kwalaben Kodin 86.

 

Babafemi ya ce nauyin kayan mayen da aka kama a gurin matashin a cikin motarsa ya kai lita 8.6.

 

Sannan ya ce hukumar ta kuma kama wasu mutane biyu a ranar 11 ga watan Yuli a Ikorodu.

 

Inda ya ce dukkan su bayan kammala bincike akansu hukumar za ta aike da su gaban kotu domin yi masa hukunci.

 

 

 

 

Jami’an tsaro a Jihar Zamfara sun samu nasarar kama wasu mutane masu tarin yawa wadanda ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne tare da masu kai musu bayanan sirri.

 

Jaridar Premium Times ta rawaito cewa ana zargin mutanen da aka kama sun dawo ne daga kasar Saudiyya bayan halartar aikin hajjin bana.

 

Jami’an sun kama mutanen ne a garuruwan Tsafe, Zurmi, Bungudu da kuma Shinkafi a Jihar Zamfara.

 

Wadanda ake zargin da ‘yan bindigar ne jirginsu ya sauka ne a filin sauka da tashin Jiragen sama na Sultan Abubakar na III da ke Jihar Sokoto.

 

Bayan faruwar lamarin a makon da ya gabata rahoton jaridar ya bayyana cewa jami’an da ke magana da yawun jami’an tsaron Najeriya ba su tabbatar da hakan ba.

 

Amma wasu majiyoyi da dama daga kwamitin aikin hajjin Jihar Zamfara sun tabbata da faruwar lamarin.

 

Inda suka bayyana cewa maniyyatan Jihar Zamfara na tashi ne a filin jiragen sama na Jihar Sokoto.

 

 

 

 

Gwamnatin Najeriya ta janye jami’an da ke kula da wasu mutane a Najeriya ciki har da wasu tsofaffin gwamnonin Kasar.

 

Jaridar Punch ta rawaito cewa shugaban ‘yan sanda na Kasa Kayode Egbetokun ya bayar da umarnin janye masu gadin tsohon Sakataren gwamnatin tarayya da tsofaffin Ministoci.

 

Umarnin janye jami’an ya shafi wadanda su ka taba zama ‘yan majalisar tarayya da kuma uwargidan tsohon shugaban Kasa Aisha Buhari da wani dan uwanta.

 

Wasikar janyewar da aka aikawa Hedikwatar yan sandan kwantar da tarzoma Mopol ta 45 a birnin tarayya Abuja ta zayyano sunayen tsofaffin Gwamnonin da suka hada da tsohon gwamnan Gombe, Bauchi, Imo Ogun da kuma Zamfara, sai tsohon Ministan harkokin ‘yan sanda da tsohon Ministan Neja-Delta da Halliru Jika.

 

Sauran sun hada da tsofaffin Ministoci na ma’adanai, kimiyya da fasaha da ayyukan wutar lantarki da kuma na kasafin kudi.

 

Umarnin na Kayode ya hada da tsohon shugaban PDP na kasa Iyorchia Ayu da kuma shugabar matan jam’iyyar APC.

 

Wasikar da aka fitar a makon da muke ciki ta bayyana cewa wajibi ne ayi gaggawar aiwatar da umarnin da aka bayar nan take.

 

 

 

 

 

Rahotanni na nuni da cewa shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Sanata Abdullahi Adamu yayi murabus daga kan mukaminsa na shugaban Jam’iyyar.

 

Jaridar Daily Trust ita ce ta tababtar da hakan a ranar Litinin.

 

Adamu wanda ya aike da wasikar murabus din zuwa ga shugaban ma’aikatan fadar shugaban Kasa Femi Gbajabiamila a yammacin ranar Lahadi.

 

Sanata Adamu wanda ya zama shugaban jam’iyyar ta APC a watan Maris din shekarar 2022 da ta gabata kuma ya yi murabus din ne a lokacin da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke halartar taron kungiyar AU a Kasar Kenya.

 

Murabus din Adamu na zuwa ne a lokacin da ake shirye-shiryen gudanar da taron majalisar kolin Kasar wato NEC a makon da muke ciki.

 

Wani makusanci ga tsohon shugaban jam’iyyar ya shaidawa Daily trust cewa Adamu ya sauka daga mukamin ne sakamakon shirin tsige shi da aka yi a taron ƙolin jam’iyyar da za a gudanar a ranar Talata da Laraba mai zuwa.

 

Ya kara da cewa bayan samun labarin wasu makusantan shugaban ƙasa guda biyu na shirin tattara sa hannun mahalarta taron domin amincewa da tsige shi,wanda hakan ya sanya yayi murabus din.

 

Ba tun yanzu ba aka samun rashin jituwa da Sanata Abdullahi Adamu bayan ya goyi bayan tsohon shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmad Lawal a lokacin zaɓen fidda gwani na jam’iyyar ta APC.

 

Bayan da shugaban ƙasar Bola Tinubu ya yi nasara a zaben su ka ci gaba da samun rashin jituwa a tsakaninsu.

 

Koda a baya bayannan sai da suka samu sabani akan shugabancin wakilan jam’iyyar a Majalisar Dattawa da Majalisar Tarayya.

 

 

 

 

 

 

Tsohon gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya soki gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf bisa sukar shirin bayar da Naira biliyan 500 na tallafin Shugaban Kasa Tinubu domin rage raɗaɗin cire tallafin man fetur a Kasar.

 

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da tsohon kwamishinan yada labaran tsohon gwamnan Muhammad Garba ya fitar a ranar Lahadi.

 

Ganduje ya ce Abba Kabir ya yi saurin kalubalantar shirin bayar da tallafin ,inda kuma ya bukace shi da ya yi koyi da gwamnan Jihar Imo.

 

Tsohon gwamnan ya kuma dora alhakin rashin ƙwarewa da rashin fahimtar wasu abubuwa a matsayin babban dalilin da ya sanya gwamnatin ta ke yin kwan gwaba kwan baya da katoɓara wajen fitar da kalamanta.

 

Sannan ganduje ya shawarci Abba da ya bi sha’anin mulkisa sannu a hankali.

 

A baya dai gwamnatin ta Kano ta yi ƙorafi kan rabon tallafin Naira biliyan 500 domin bai’wa ‘yan Jihar.

 

Gwamnatin ta Kano na ganin a gurin rabon tallafin an fifita wasu Jihohin akan wasu.

 

Bayan kalaman na gwamnatin ta Kano aka buƙace ta da jam’iyyar ta NNPP da su samar da ingantaccen shiri wanda zai rage raɗaɗin da mutanen Jihar su ke ciki ba su ringa neman makusa ba a shirin gwamnatin tarayya na rage raɗaɗin tallafin man fetur.

 

Amma a yayin kalaman gwamnatin ta Kano ta yi watsi da Rahoton cewa ta soki gwamnatin tarayya kan rabon tallafin Naira biliyan 500,inda ta ce ba a fahimci Kalaman da ta yi ba akan tsarin rabon tallafin domin ragewa ‘yan kasar radadin cire tallafin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: