Yau Laraba musulmi a fadin Najeriya ke murnar zagayowar sabuwar shekarar hijira.

Sarkin musulmi a Najeriya Alhaji Saad Abubakar lll ne ya ayyana yau Laraba a matsayin ranar farko na sabuwar shekarar hijira ta 1445.

Sanarwar hakan na zuwa ne bayan da aka gaza ganin sabon jinjirin watan a ranar Litinin.

A Najeroya shugaban kasar Bola Ahmed Tinubu ya taya daukacin musulmi murnar sake zagayowar sabuwar shekarar hijira.

Kuma ya bukaci yan kasar da su yi amfani da ranar don yin addu’a bisa mawuyacin halin da kasar ke ciki.

Wasu daga cikin gwamnonin Najeriya sun bayar da hutu a yau don murnar sake zagayowar sabuwar shekarar hijira.

Leave a Reply

%d bloggers like this: