Gwamnatin jihar Kafuna ta ce akwai talakawa masu karamin karfi miliyan 3.9 a jihar.

Mataimakiyar gwamnan jihar Dakta Hadiza Sabuwa Balarabe ce ta bayyana haka yauin rufe wani taro da kungiyar Action Aid of Nigeria ta shirya don bayar da gudunmawa ga marasa karfi a jihar.
Dakta Hadiza Sabuwa wadda ta samu wakilcin mataimakin shugaban maaikatanta, ta ce jihar Kaduna akwai magidanta sama da miliyan daya da ke fama da talauci.

Sai mataimakiyar gwamnan ta yaba ga irin kokarin aikin kungiyar na tallafawa marasa galihu a jihar.

Sannan ta tabbatar da cewar gwamnatin jihar a shirye take don ganin ta hada kai da kungiyoyi don cika muradin da ta saka a gaba.
Gwamnatin ta ce jihar na da mutane da ke fama da talauci miliyan 3.9 yayin da a kananan hukumomi 23 na jihar akwai magidanta da ke fama da talauci sama da miliyan ɗaya.