Majalisar wakilai a Najeriya ta yi watsi da kudirin da za a hana kara farashin litar mai a kasar.

 

A zaman majalisar na yau Laraba sun ce an kafa kwamiti da zai duba tare da bincike don gano dalilin sake kara farashin litar man.

 

Kara farashin kitar man fetur ya haifar da tsadar sufuri baya ga wadda ake fama da ita a baya.

 

Wani dan majalisa mai suna Ikenga Ugochinyere ne ya bukaci majalisar ta gayyaci shugaban kamfanin mai na Najeriya Malam Mele Kyari don bayani a dangane da karin farashin litar man.

 

Sai dai kwamitin da aka kafa a majalisar tarayyar ya mayar da hankali ne wajen ganin yadda za a raba tallafon da gwamnatin kasar ta ware na naira biliyan 500 don rage radadin cire tallafin man fetur.

 

Fatashin litar mai ya yi tashin gwauron zabi daga naira 185 zuwa naira 540 tun bayan da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayyana rashin amincewa da cigaba da bayar da tallafin a gwamnatinsa, yayin da yake jawabi Jim kadan bayan rantsar da shi a matsayin sabon shugaban Najeriya.

 

Kuma a ranar Talata farashin ya sake tashi zuwa nakra 617 zuwa naira 630 kan kowacce lita.

 

Ko da yake kamfanin mai na Najeriya NNPC ya ce za a dinga fuskantar hawa da saukar farashin man fetur lokaci zuwa lokaci, kasancewar gwamnatin ta zare hannunta a kai.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: