Gwamnan Jihar Sokoto Ahmad Aliyu ya mika sunayen kwamishinoni 16 ga majalisar dokokin Jihar.

 

Sanarwar mika sunayen na kunshe ne cikin wata takarda da gwamnan ya aike wa shugaban majalisar dokokin Jihar Alhaji Tukur Bala wanda ya karanto a zauren majalisar a ranar Alhamis.

 

Gwamnan ya ce nadin mutanen ya biyo bayan tuntuba da kuma bin matakan da suka dace kamar yadda yake a cikin dokokin aikin gwamnatin.

 

Shugaban majalisar Tukur Bala ya shaidawa mambobin majalisar cewa majalisar za ta tantance waɗanda aka zaba a ranakun 2 da 3 ga watan Agusta mai kamawa.

 

Gwamnan ya ce nadin nasu yazo ne a tanadin sashe na 192 da sauran sassan da suka dace na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 da aka yi wa kwaskwarima kan nadin kwamishinoni.

 

Daga cikin kwamishinan da gwamnan zai nada sun hada Jamilu Gosta, Bashar Umar,Dakta Jabir Mai-Hulla,Balarabe Kadadi,Isa Tambagarka, Aliyu Tureta, Hadiza Shagari, Asabe Balarabe ,Bello Wamakko.

 

Sauran su ne Tukur Alkali, Bala Kokani, Aminu Abdullahi, Mohammed Shagari,Nasiru Aliyu ,Ya’u Danda,da kuma Yusuf Maccido.

 

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: