Rundunar yan sanda a jihar Anambra sun samu nasarar kama wasu da ake zargi da aikata fashi da makami a jihar.

An kama mutane biyu daga ciki bayan an kai farmaki a maboyarsu.


Mai magana da yawun yan sanda a jihar Tochukwu Ikenga ya shaida cewar sun yi hadin gwiwa ne da yan sa kai a jihar.
Sannan sun kwato makamai yayin da su ka kai farmakin daga cikin abubuwan da su ka samu akwai bindigu kirar gida da na waje.
Jami’in ya ce sun smau bayanai a kan maboyar ne bayan sun kama guda cikin jagororinsu a ranar 11 ga watan Yuli da mu ke ciki.
Kwamishinan yan sandan jihar ya yabawa jami’an sa kai da sauran yan sanda da su ka tabbatar da nasarar.
Mutanen da aka kama su kae zargi da addabar wasu yankuna a jihar da aikata fashi da makami da sauran laifuka.