Kungiyar Kiristoci a Najeriya CAN ta jinjimawa shugaban Kasa Bola Tinubu bisa kokarin da yake yi wajen ganin ya dawo da mulkin dimokuraɗiyya a Jamhuriyyar Nijar.

Shugaban kungiyar na ƙasa Archbishop Daniel Okoh ne ya bayyana hakan ta wani saƙo da ya aikewa da Tinubu da kungiyar ta ECOWAS.

Daniel ya ce kungiyar ta su ta goyi bayan duk wani kokarin da ake yi na dawo da dimokuraɗiyya a Nijar,inda ya ce kungiyarsu ba ta goyi bayan amfani da ƙarfin soji ba a Kasar.

CAN ta ce yin amfani da karfin soji zai iya haifar da kiyayya da gaba mai tsanani a tsakanin Najeriya da jamhuriyyar ta Jihar.

CAN ta kuma yi kira ga Tinubu da ya bi duk wasu hanyoyi da suka dace domin samar da maslaha domin ganin ya kawo karswhen rikicin ba tare da yin abinda zai ɓata alaƙar ƙasashen.

Kungiyar ta kuma yabawa ECOWA akan yin adawa da juyin mulkin Nijar da take yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: