Shugaban gwamnatin sojin Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahamane Tchiani ya nada ministoci 21 karkashin jagorancin sabon Fira Ministan kasar.

Shugaban ya bayyana haka ne a ta cikin wata sanarwa da ya fitar ta kafar talabijin na Kasar a ranar Laraba.
Abdourahamani ya ce sun nada ministocin ne domin kara tabbatar da karfin ikonsu a cikin kasar a lokacin da su ke fuskantar barazana daga wasu kasashe akan juyin mulkin da su ka yi.

Shugaban gwamnatin Kasar ya kara da cewa sabon Fira Minista Ali Mahaman Zeine Lamine shine zai jagoranci gwamnatin mai mambobi 21 daga jiya Laraba.

Daga cikin ministocin da aka nada ciki harda na tsaro da ministan harkokin cikin gida guda biyu.
Gwamnatin kasar Nijar na cigaba da fuskantar matsin lamba daga ƙungiya ECOWAS da sauran ƙasashen duniya bayan juyin mulkin daa su ka yi a ƙasar.