Ƙungiyar bunƙasa tattalin arziƙi ƙasashen Afrika sun umarci sojoji da su fara shiri don fara kai hari Nijar.

Majalisar ƙoli ta ƙungiyar ce su ka cimma matsayar haka a zaman da su ka yi yau a Abuja bisa jagorancin shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Hakan na zuwa ne yayin da shugabannin soji a jamhuriyar Nijar ke cigaba da naɗa muƙamai a ƙasar wanda ƙungiyar ta ce hakan babbar barazana ce ga ƙasar.

Ƙasashen da su ka zauna don zartar da hukuncin a yau sun goyi bayan amfani da soja wajen ƙwace mulki daga hannun sojin Nijar.

Sojin jamhuriyar Nijar sun bayyana aniyar mayar da martani ga duk ƙasashen da su ka yi yunƙurin kai musu hari da nufin ƙwace mulki.
Tuni su ka bayar da umarnion rufe iyakokin sama da na ƙasa a ƙasar don cigaba da mulkin soji.
Ƙasashen Mali da Burkina Faso za su aike da dakarunsu jamhuriyar Nijar a ranar Litinin mako mai zuwa.
Kamar yadda Mujallar Matashiya ta ruwaito, a zaman majalisar ƙoli na ƙungiyar ECOWAS da ya gudana a yau, sun buƙaci tallafin tarayyar Turai a kan hukuncin da su ka yanke.