Gwamnatin Jihar Jigawa ta shirya rabon bayar da tallafi domin rage radadin cire tallafin man fetur ga al’ummar Jihar.

Kwamishinan yada labarai, harkokin matasa, wasanni da al’adu a Jihar Sagir Musa, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Kwamishinan ya ce an cimma matsayar ne bayan wani zama da majalisar zartaswar jihar.

Sagir ya kara da cewa gwamnatin jihar ta amince da fitar da Naira miliyan 134 domin siyo tirelolin shinkafa guda biyar tare da raba wa masu ƙaramin ƙarfi a Jihar.

Kwamishinan ya ce majalisar ta kuma amince da shirin bayar da tallafi ga matasa masu kananan sana’o’i 1,500 a cikin ƙananan hukumomi 27 na jihar.

Musa ya kara da cewa kowane daga cikin masu kananan sana’o’in za su amfana da Naira 50,000 domin su kara karfin jari a cikin kasuwancin nasu.

Shirin zai gudana ne a ƙarƙashin ma’aikatar yada labarai matasa wasanni da al’adu tare da hadin gwiwar hukumar samar da ayyukan yi da dogaro ga kai ta Jihar.

Kazalika ya ce majalisar ta amince da bayar da tallafin naira 100,000 ga kanana da matsakaitan yan kasuwa 1000 ta hanyar shirin ‘J-Cares’ wanda babban bankin duniya yake bayar da tallafi a kai.

Sannan ya bayyana cewa masu kananan sana’o’in da suka cika sharuɗɗan bankin duniya na samun asusun ajiyar lambar BVN da akalla ma’aikata biyu a karkashin su ne za su amfana da tallafin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: