Helkwatar tsaro a Najeriya ta ce ba ta da shirin yin juyin mulki a ƙasar kamar yadda wasu ke zargi.

 

Helkwatartar ta musanta batun yin juyin mulki a Najeriya tare da cewar waɗanda ke da tunanin haka a ransu za su sha kunya.

 

Helkwatartar ta ce ta samu wasika daga wasu da ba su san su waye ba kan buƙatar yin juyin mulki a Najeriya kamar yadda aka yi a makofciyar kasar.

 

Buƙatar tumbuke mukin shugaba Bola Ahmed Tinubu da aka aike da wasikar mutanen sun ɗora alhakin rashin walwala da jami’an ke ciki.

 

Daraktan yaɗa labarai na helkwatar tsaro Birgediya Tukur Gusau ya tabbatar da lamarin a shafin hukumar na twitter.

 

Su ka ce an yi kira garesu da su juyar da buƙatar amfani da su a jamhuriyar Nijar zuwa juyin mulki a Najeriya wanda su ka ce ba su da niyyar yin haka.

 

Helkwatar ta ce za ta ci gaba da biyayya ga kundin tsarin mulki a Najeriya tare da tabbatar da cigaban demokradiyya.

 

Hakan na zuwa ne bayan da sojoji su ka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijar a ranr 26 ga watan Yuli da ya gabata.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: