Wasu da ake zargi mayakan ƙungiyar Boko Haram ne sun budewa wasu masu matafiya da fasinjoji wuta a jihar Borno.

Lamarin ya faru a karamar hukumar Bama ta jihar.


Maharan sun kashe kalla mutane biyar sannan su ka tafi da wasu mata bakwai.
A tsakar ranar Alhamis mutanen a cikin mota da fasinjoji bisa rakiyar jami’an tsaro su ka faɗa tarkon mayakan Boko Haram a garin Banki iyaka da kasar Kamaru.
Wani cikin mutane da ke ta’ammali da hanyar mai suna Babagana Kuami ya shaida cewar mayakan sun farwa matafiyan ne a garin Banki da ke ƙaramar hukumar Bama.
Ya ce hare-haren mayakan Boko Haram ya tsananta a garuruwan da ke iyaka da Kamaru.
Sai dai har zuwa yanzu jami’an tsaro ba su ce komai a kan lamarin ba.
Idan ba a manta ba a jiya juma’a rundunar tsaron Najeriya ta ce ta hallaka ƴan ta’adda da kama masu garkuwa da mutane da kuma kuɓutar da mutanen da aka kama, har ma ta ce ta kwato makamai daga hannun bata gari a sassa daban-daban na ƙasar.