Rahotanni daga birnin Zaria a jihar Kaduna na nuni da cewa mutanen da su ka rasa rayuwarsu sakamakon ruftawar babban masallacin garin sun kai su 11.

 

Sannna an gano mutane 20 da su ka samu rauni daban-daban a sakamakon rushewar masallacin.

 

Masallacin ya rushe a kan mutane yayin daa ake tsaka da salla a ranar Juma’a.

 

Mai magana da yawun masarautar Zazzau Malam Abdullahi Aliyu Kwarbai ya bayyanawa ƴan jaridaa cewa, waɗanda aka hako gawarsu an sallacesu a daren ranar Juma’a.

 

Ya ce an cigaba da hako gawarwakin mutanen bayan da ginin masallacin ya rufta a kansu.

 

Saarkin Zazzau ya aike da tawaga domin duba waɗanda lamarin ya rutsa da su.

 

An gina masallacin tun a shekarar 1830 wanda yaa zamto babban masallaci a birnin Zaria.

 

Sarkin Zazzau Ambasada Nuhu Ahmed Bamalli ya aike da sakon jaje ga iyalan mutanen da su ka rasa rayuwarsu.

 

Haka zalikaa gwamnatin jihar Kaduna ta aike da sakon taaziyya ga iyalna waɗanda su ka rasa ƴan uwansu tare da alƙawarin yin bincike a kan dalilin rushewar ginin masallacin.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: