Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya ce za su yi aiki da kafaɗa da kafaɗa da ministocin sa don ganin an cikawa ƴan ƙasar alƙawuran da aka ɗaukar musu.

Tinubu ya bayyana haka ne jim kaɗan bayan rantsar da sabbin ministocin da ya bai naɗa a ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Ya ce ya ba su muƙaman ne domin ya yarda da jajircewarsu kuma ya tabbata za su taimaka masa wajen fita kunyan ƴan Najeriya.

Sannan ya horesu da kowa ya tsaya a kan aikinsa tare da farawa ba tare da ɓata lokaci ba domin fita kunyar ƴan ƙasar.
Shugaba Tinubu ya buƙaci haɗin kan ministocinsa ta yadda za a samar da cigaba mai ɗorewa a faɗin ƙasar.

An rantsar da ministoci 45 a Najeriya wanda hakan ke alamta fara aiki tuƙuru domin dafawa gwamnatin tarayya a matsayinsu na ƴan majalisar zatarwa.

An zaɓo ministocin ne daga kowace jiha a faɗin Najeriya, kamar yadda kundin tsarin mulki ya bayar da dama.

 

Leave a Reply

%d bloggers like this: