Gwamnan Jihar Adamawa Ahmadu Fintiri ya kafa wani kwamiti mai dauke da mutune 20 domim raba kayan tallafin ga mutanen Jihar domin rage musu radadin halin da su ke ciki.

Mai magana da yawun gwamnan Humwashi Wonosikou ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar.
Kakakin ya ce mambobin kwamitin sun fito ne daga kungiyoyi ma’aikatu da kuma daidaikun jama’a.

Kazalika ya ce mafi yawa daga cikin kayan da kwamitin zai raba a matakin farko kayan abinci ne.

Gwamnan zai rantsar da kwamitin da gwamn ranar Talata mai zuwa domin ganin an ragewa mazauna Jihar radadin halin da suke ciki.