Shugaban ƙungiyar kimiyyar lafiyar muhalli a Najeriya Godson Ana ya ce aƙalla mutane sama da 400,000 ne ke rasa rayuwarsu a sanadin zazzaɓin cizon sauro a duniya.

Sannan akwai mutane sama da miliyan 219 da ke fama da cutar zazzaɓin cizon sauro a faɗin duniya baki ɗaya.
Farfesa Godson Ana ya bayyana haka ne a yayin jawabin da ya gudanar ranar Litinin a matsayin ranar sauro ta duniya.

Taken taron shi ne yaƙi da kisa dalilin zazzaɓin cizon sauro a duniya wanda aka yi ranar Litinin a Abuja.

Ya ce mafi yawan mutanen da ke mutuwa sanadin zazzaɓin cizon sauron yara ne da ke tsakanin shekara biyar zuwa ƙasa.
Sai dai Farfesa Godson Ana ya bayyana yaɗuwa nau’i daban-daban na sauro wanda ya ce akwaisu da ke cigaba da wanzuwa a doron ƙasa.
Kuma ya bayar da shawara dagewa da tsaftace muhalli, rashin tsaftace muhallin na iya haifar da yawaitar sauro wanda ke illa ga lafiya ko ma sanadiyyar rasa rayuwa baki ɗaya.