Shugaban Najeriya kuma shugaban ƙungiyar ECOWAS Bola Ahmed Tinubu ya gana da masu ruwa da tsaki a kan tsaron don tattauna batun da ya shafi jamhuriyar Nijar.

Jagoran kwamitin sulhu tsakanin ECOWAS da shugabannin mulkin sojin Nijar Janar Abdussalam Abubakar mai ritaya na daga cikin waɗanda su ka halarci zaman na yau a Abuja.
Ya ce sun isar da saƙon da shugabannin mulkin sojin Nijar su ka bayar, bayan dawowarsu domin shiga tsakani yayin da ƙungiyar ECOWAS ke fafutuka don ganin an dawo da mukin demokaraɗiyya a ƙasar.

Ya bayyana cewa tsarin diplomasiyya zai yi aiki matuƙa wajen sasantawa ba tare da an shigar da yaƙi don dawo da mulkin farar hula a ƙasar ba.

su ka yi da masu mulkin sojin jamhuriyar Nijar bayan wakilcin da su ka yi don sasantawa.
Haka kuma akwai kyakkyawan sakamako da za a gani ba da jimawa ba.
Shugabannin mulkin soji a jamhuriyar Nijar dai sun bayyana aniyar miƙa mulki ga farar hula zuwa shekaru uku masu zuwa..
Batun da ƙungiyar ECOWAS ta yi watsi da shi.
