Rundunar sojin ta Operation Hakorin Damisa IV sun samu nasarara kama mutane 39 da ake zargi da alaƙa da ƴan fashi, garkuwa da mutane da kuma fashi da makami a jihar Filato,

An kama mutanen tare da gano wasu makamai da ƙwayoyi daga wajensu.
Mai Magana da yawun rundunar ta Operation Haƙorin Damisa Kaftin Oya James ya bayyana haka jiya Talataa wata anarwa day a aikewa manema labarai.

Ya ce sun samu nasarar ne bayan yin aikin haɗin gwiwa da sauran jami’an tsaro.

A cikin sanarwa ya ce an ƙwato bindiga ƙirar AK47 guda da sauran makamai daga hannun mutanen da ake zargi.
Daga cikin mutanen da aka kama akwai wani da ake zargi babban dilan makamai ne da ke rabawa masu garkuwa da mutane kuma an kamashi a ƙauyen Kuba da ke ƙaramar hukumar Bokkos a jihar Filato.
Sannan sunkuɓutar da wasu shanu da yawansu ya kai 307.
Kuma an kuɓutar da mutane 17 da ake zargi an yi garkuwa dasu daga hannun mutanen da aka kama.