Hukumar lafiya a Najeriya na duba yuwuwar ƙara harajin lemon kwalba da na roba a ƙasar.

Hukumar na son ƙara harajin ya koma kashi 20 maimakon kashi goma da ake karɓa a yanzu.
Hukumar ta ga dacewar ɗaukar matakin hak ane domin rage amfani da suga da mutane ke yi.

Ƙasashe da dama sun mayar da harajin zuwa kashi 20 kamar yadda hukumar lafiya ta duniya ta aminta da haka.

Hukumar ta ce ana samun yawan masu cutar siga, hakori, da sauran cutuka da ke da alaƙa da suga wanda hakan ke zama barazan aga lafiya da rayuwar jama’a.
Kuma an ɗauki matakin haka ne domin rage amfani da kayan lemo masu zaki wanda mutane ke amfani da shi a yau da kullum.
Dakta Chukwuma Anaike da ke zama daraktan hulɗa da jama’a na hukumar shi ne ya bayyana haka a wani zama da hukumar lafiya haɗin gwiwa da hukumar gudanarwar kuɗi na ta ƙasa su ka yi a yau Talata.
Ya ce an dauki matakin ne ganin hatsarin da ke tattare da amfani da siga domin ɗaukar mataki.
Hukumar ta gano yadda ake samun yara ƙanana ɗauke da ciwon siga da sauraan cutuka masu alaƙa da ta’ammali da siga.