Ƙungiyar kare haƙkin musullmi a Najeriya MURIC ta yi kira ga sojojin ƙasar da kada su yi koyi da sojin ƙasar Gabon da su ka yi juyin mulki a yau.

Shugaban ƙungiyar Farfesa Akintola Ishak ne ya shawarci sojin a yau bayan da sojoji su ka sanar da hamɓarar da shugaban Ali Bongo.
A wata wasiƙa da ƙungiyar ta fitar, ta ce dukkan wani sojan ƙasar da ke ƙoƙarin kwaikwayon sojin Gabon na yi ne domin son zuciya.

Ƙungiyar ta ce akwai bambanci mai yawa tsakanin yan siyasar Gabon da na Najeriya.

Sannan ta ce dukkanin wanda ke ƙoƙarin yin juyin mulki kai tsaye ya na yaƙar musulunci ne ganin yadda shugaba da mataimakinsa duka musulmi ne.
Ƙungiyar ta fahimci a wannan lokaci sojojin Najeriya na mayar da hankali wajen samar da zaman lafiya a wajen da ƴan ta’adda su ka addaba.
Sannan ta yi kira ga sojojin ƙasar da sun ci gaba da mayar da hankali wajen ayyukan da su ke yi kamar yadda aka sansu bayan samun ingantaccen horo a Najeriya.