Masu sana’ar rini a jihar Ogun sun yi kira ga gwamnan jihar da ya dakatar da siyar da kayan da aka rina wanda aka shigo da shi daga ƙasar China.

Ƴan kasuwa da masu sana’ar rinin sun koka kan cewar hakan na iya dakushe harkokin kasuwancinsu da kuma durƙusar da sana’ar.

Mutanen sun fahimci shigo da kayan da aka rina zai iya rusa sana’ar rini a jihar da kuma lalata kasuwanci.

Guda cikin ƴan kasuwar da ya yi wa yan jarida jawabi Ogunfidodo Micheal ya ce sun bai wa waɗanda ke siyarwar wa’adi don ganin sun ƙarar da kayansu.

Sannan ya zargi cewar hakan na iya jefa matasa da dama a jihar cikin rashin aikin yi kuma barazana ce a garesu.

Sannan ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta dawo da masa’antun sarrafa tufafi na gida domin tallafar masu ƙananan sana’o’i a ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: