Gwamnatin jihar Sokoto ta ware kudi kimanin naira biliyan 4 don siyan kayan abinci da za a raba a fadin kananan hukumomi dake jihar.

Jaridar Punch ta ruwaito, cewa wannan na daga cikin kokarin da gwamnatin jihar ke yi don ragewa al’ummar jihar radadin cire tallafin man fetur.


Da yake jawabi ga manema labarai a zauren majalisa bayan taron majalisar zartarwa na jihar a ranar Juma’a, 1 ga watan Satumba, kwamishinan harkokin addini, Sheikh Dr Jabir Maihula, ya ce gwamnan jihar, Ahmed Aliyu Sokoto, ya amince da siyan kayayyaki don rabawa al’umma mabukata.
A cewar kwamishinan mambobin majalisar zartarwa na jihar a taronsu sun amince da siyan buhuhunan shinkafa yan 50kg guda 57,000 kan kudi naira biliyan 2.508.
Majalisar ta kuma amince da siyan wasu buhuhunan gero yan 100kg guda 26,000 kan kudi naira biliyan 1.430.
Sannan ya yi bayanin cewa gwamnan ya kafa wani kwamitin da zai kula da rabon kayan abinci a fadin kananan hukumomi 23 na jihar.
Punch
