Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya tabbatarwa da yan Najeriya ƙudirinsa na tabbatar da Najeriya a matsayin ƙasa mai ingantaccen zaman lafiya da cigaba.

 

Tinubu ya bayyana hakan ne a wani jawabi da mai magana da yawunsa, Ajuri Ngelale ya sanyawa hannu bayan hukuncin da kotu ta yanke kan ƙarar da aka shigar na ƙalubalantar cin zaben shugaban kasar.

Alkalai guda biyar da su ka jagoranci shari’ar, sun kori ƙarar da dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar da na Peter Obi na Labour Party su ka shigar gabanta.

 

Da ya ke yanke hukunci jagoran alkalan, Haruna Simon Tsammani ya ce Bola Ahmad Tinubu ne ya lashe zaben shugaban kasar wanda aka gudanar a watan Fabarairu na wannan shekara.

Ngelale ya ce shugaba Tinubu ya yi maraba da hukuncin sannan ya godewa dimbin alummar Najeriya bisa irin goyon baya da adduoinsu kan shariar.

 

Ya ƙara da cewa irin yadda hukuncin ya kasance ya nuna ƙarara yadda ɓangaren Shari’a a ƙasar su ke gudanar da aikinsu cikin kwarewa, wanda hakan ke sake fito da martabar Najeriya tare da kare matsayinta na kasar da ta fi girma a nahiyar Afrika.

Leave a Reply

%d bloggers like this: