Kwamishinan kula da kasa a jihar Kano Adamu Aliyu Kibiya, ya yi barazana ga alkalan kotun sauraron kararrakin zaben gwamna.

Sannan kuma ya yi alkawarin tayar da rikici ga mazauna jihar, fiye da rikicin da al’ummar makotan jihar na jihohin Kaduna da Zamfara su ke fuskanta.

Mazaunan jihohin Kaduna da Zamfara dai su na fuskantar tashin hankalin hare-hare, kisa, da kuma garkuwa da su don karbar kudin fansa daga ‘yan bindiga.Wannan hare-haren dai yana faruwa sama da shekaru 10.

Aliyu ya yi zargin cewa, da akwai yiwuwar an bai wa alkalan cin hanci da rashawa dan su yi hukuncin da ba zai yi wa jam’iyyarsa dadi ba.

Kwamishinan ya yi barzanar cewa, idan alkalan kotun su ka yi hukuncin da bai bai’wa jam’iyyarsa ta NNPP nasara ba a korafin dake gabanta, to zasu biya bashin hakan da rayuwarsu.

Jam’iyyar APC da dan takarar gwamnanta Nasiru Yusuf Gawuna dai, su na kalubalantar nasarar da gwamnan jihar ta Kano Abba Kabir Yusuf ya samu a zaben da ya gabata.

Kotun sauraron kararrakin zaben dai har yanzu ba ta sanya ranar da za ta yanke hukunci a kan shari’ar ba, yayin da Aliyu Adamu ya yi wannan ikirarin lokacin da yake jawabi ga magoya bayan jam’iyyar NNPP yayin wata zanga-zanga da suka gudanar a ranar Alhamis.

Taron da aka gudanar kuma ya hadar da yin addu’a, don fatan yin nasara ga tsagin nasu a hukuncin da za a yanke.

Leave a Reply

%d bloggers like this: