Kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan jihar Kano ta shirya tsaf domin yanke hukunci kan ƙarar da jam’iyar APC ta shigar na kalubalantar nasarar da jam’iyyar NNPP ta samu.

Cikin wata sanarwa da babban rijistara na kotun sauraron ƙararrakin zaben ya fitar a yammacin jiya Litinin, ta bayyana cewa za a yanke hukuncin ne a gobe Laraba 20 ga watan Satumban na wannan shekara, karkashin jagorancin justice Oluyemi Akintan.


Tun a watan Maris na wannan shekara ne dai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta ayyana Engr Abba Kabir Yusuf a matsayin aanda ya lashe zaben da kuria miliyan daya da dubu sha tara da dari shida da biyu.
Inda ya kada abokin karawarsa Dr Nasiru Yusuf Gawuna wanda ya samu kuria dubu dari takwas da casain da dari bakwai da biyar.
Gabanin yanke hukuncin zaben dai, jamiya mai mulki da mabiya darikar Kaankwasiya da kuma magoya bayan jam’iyar adawa ta APC sun gabatar da salloli da adduoi a wurare daban daban da nufin samun nasara.
Daya daga cikin alkalan da za su jagoranci yanke shariar a gobe mai sharia Osadebayo, ya tabbatar da yin adalci a tsakanin jamiyun biyu kamar yadda hurumin doka ya tanadar.