Rundunar tsaron haɗin gwiwa a jihar Kaduna sun samu ansarar gano wani gida da ake haɗa bindigu da sauran makamai.

An gano gidan a Kafanchan da ke ƙaramar hukumar Jema’a a jihar.

Yayin sumamen da su ka kai sun gano bindigu ƙirar AK47 da wasu injina da su ke aikin haɗa makaman da su.

Sannan sun gano kayan jami’an soji, da na ƴan sanda.

Makaman da ake haɗawa ana amfani da su ne wajen haddasa rikici a jihohin Kaduna da Filato a cewar jami’an tsaron.Kafanchan a jihar Kaduna.

Rundunar ta ce ta kama wasu muggan makamai da kayan jamian ƴan sanda da soji a ƙauyen Adua da ke ƙaramar hukumar

Babban kwamandan runduna ta uku Manjo Janar Abdussalam Abubakar ya yabawa jami’ansa sannan ya sha alwashin gurfanar da waɗanda aka kama a gaban kotu domin fuskantar hukunci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: