Mai dakin shugaban kasa Bola Tinubu Remi Tinubu ta bayyana cewa gwamnatin shugaba Bola Tinubu ta mayar da hankali ne akan gyaran matsalolin da suka addabi Kasar.

Remi ta bayyana haka ne a yayin da ta halarci coci domin yin addu’o’i da kuma bikin cikar Kasar shekaru 63 da samun ‘yancin kai a ranar Lahadi.
Uwar gidan shugaban ta ce mai gidan ta ya tarar da tarin matsaloli masu yawa daga gwamnatin da ya gada.

Remi ta kara da cewa duk da tarin matsalolin da mai gidan ta ya gada, ya kuduri aniyar shawo kan matsalolin da kasar ke fuskanta.

Kazalika ta ce Tinubu zai yi kokari wajen ganin ya gyara dukkan kurakuran da ya tarar a cikin kasar.
Sannan ta ce nan ba da jimawa ba ‘yan Kasar za su dawo cikin walwala da jindadi daga cikin halin matsin da suka tsinci kansu.