Gwamnatin tarayya ta ce mutane a ƙasar za su fara samun fasfo dinsu na ƙasa da ƙasa cikin makonni biyu kacal bayan sun bayar da bayanansu.

Ministan harkokin cikin gida Olubunmi Tinji-Ojo ne ya bayyana haka yau a Abuja.

Ya ce mutane a ƙasar ba za su haura makonni biyu ba ba tare da sun smau fasfo dinsu na tafiya ba daga yanzu.

Zuwa yanzu hukumar shige da fice a Najeriya NIS ta kammala aikin fasfo na mutane 204,332 da ba a kammala ba a baya.

Hakan na zuwa ne bayan da linistan ya bayar da umarni a ranar 7 ga watan Satumba cewa hukumar ta gaggauta kammala aikin fasfon da ke hannu cikin makonni biyu.

Ministan ya tabbatar da cewar daga yanz ba za a sake samun tsaiko wajen aikin fasfo ba.

Sannan mutane a yanzu na iya aike da bayanansu a yanar gizo, abu guda da zai kai su zuwa ofishin hukumar shi ne daukar hoton yatsa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: