Kimamin dalibai guda biyar ne ‘yan mata na jami’ar gwamnatin tarayya da ke Dutsin-Ma a jihar Katsina, aka sace daga wadanda ake zargin ‘yan ta’addah ne. Sakamakon tabbatar da hakan da hukumar ‘yan sanda suka yi bayan an kama wani mutum guda daya da ake zargi da aikata laifin.

An bayyane cewa wadanda ake zargin abin ya rutsa da su, an yi garkuwa da su ne a mazaunansu. Da suke zaune a bayan makarantar Mariamah Ajiri da ke kan titin Tsaskiya a jihar ta Katsina.

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa, an sace daliban ne a daidai 2:30 na daren ranar jiya.

An tuntubi mai magana da yawun rundunar ‘yan sandar jihar ASP Abubakar Sadiq, kuma ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya kuma bayyana cewa an damke daya daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifin, ya kara da cewa har yanzu suna kan bincike akan lamarin bisa kokarinsu na ceto ‘yan matan daga hannun bata garin.

“Eh lamarin ya faru da gaske, kuma tuni mun cafke mutum guda daga cikin wadanda ake zargi, muna kan bincike akan lamarin dan shawo kan matsalar.” Abubakar ya fada.

Leave a Reply

%d bloggers like this: