An rasa rayukan kimanin mutane 40 a jihar Sikkim ta ƙasar Indiya, biyo bayan samun ruwan sama mai ƙarfi jihar da take Arewa maso Gabashi.

Samun ruwan ya yi sanadiyyar haifar da ambaliyar ruwa daga tafki mai dauke da ruwan sanyi, wanda ta mamaye yankin da ambaliyar ruwan sanyin.
Ambaliyar ta kasance ɗaya daga cikin mafi munin annoba da aka samu a yankin cikin shekaru 50, ta shafe gidaje da gadoji, kuma ta tilastawa dubbannan mutane barin muhallansu a ranar Laraba.

Yanayin ya zamo silar lalacewar manyan gine-gine, sannan cigaba da aka yi da mamakon ruwan ya sanya aikin ceto rayuka ya yi matukar wahala.

Gwamnatin ƙasar ta Indiya ta sanar da cewa, ambaliyar ruwan ta shafe gadoji guda 15. Ciki har da gadojin da ke ƙarƙashin babbar tashar samar da wutar lantarki ta Teesta-V.
Babban sakataren jihar ta Sikkim Vinay Phatak a yau Juma’a ya bayyana cewa, suna aikin fitar da mutane bisa amfani da jirgi mai saukar ungulu, wanda rundunar sojojin ƙasa da ta sama su ka samar.
Kimanin mutane 2,400 dai aka ceto tun daga ranar Laraba, yayin da mutane 27 su ka samu raunuka kuma aka garzaya da su asibiti.
Masu aikin ceto dai har yanzu suna ƙoƙarin gano mutane 100 da su ka ɓace, ciki har da jami’an sojojin 23.
Manyan jami’an maƙociyar jihar da ga yammacin Bengali sun sanar da wakilan Reuters cewa, jami’an bayar da agajin gaggawa sun gano gangar jikin mutane 22 da ambaliyar ruwan ta shafe.