Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Ola Olukayede, a matsayin shugaban hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta EFCC.

Domin yin aiki a matsayin shugaban hukumar na tsawon shekaru huɗu, wanda yanzu haka yake jiran tabbatarwa daga majalisar dattijai.

Mai magana da yawun shugaban ƙasar Ajuri Ngelale ya sanar da hakan a yau Alhamis.

Ya kuma ce naɗin na Olukayede ya biyo bayan ajiye aiki, da dakataaccen shugaban hukumar AbdulRashid Bawa ya yi.

Ya ce haka zalika kuma shugaba Tinubu ya amince da naɗin Muhammad Hassan Hammajoda, a matsayin magatakardar hukumar, wanda zai yi aikin tsawon shekaru biyar da yanzu haka yake jiran tabbatarwa daga majalisar dattijai.

Ngelale ya ce naɗe-naɗen an yi su ne bisa doron ikon da doka ta baiwa shugaban kasa, wanda take sashi na 2(3) na dokar da ta ƙirƙiri hukumar ta EFCC a shekara ta 2004.

Leave a Reply

%d bloggers like this: