An sake cafke tsohon shugaban gwamnatin soji ta ƙasar Gini Moussa Dadis Camara a jiya Asabar, bayan ya tsere daga babban gidan yari a Conakry babban birnin ƙasar.

Shugaban sojojin ƙasar ta Gini Ibrahima Sory Bangoura ya tabbatar da hakan, ya kuma ce Camara yana cikin ƙoshin lafiya, kuma an mayar da shi gidan yarin na Conakry.

Ya kuma ce an kuma cafke mutane biyu da suka tsere tare da shi, wato Moussa Tiegboro Camara da Blaise Gomou. Kuma an mayar da su gidan yarin su ma.

Sannan sojojin sun bayyana cewa, ana ta ƙoƙari don ganin an kamo ragowar ɗayan da suka tsere tare, wato Claude Pivi.

Kotun ɗaukaka ƙara a ƙasar wacce ta ke a Conakry, ta bayar da umarnin a yi cajin su da babban laifi dukka su huɗun.

Moussa Camara dai ya Ƙaddamar da juyin mulki a ƙasar, ranar 23 ga watan Disambar shekerar 2008. Wanda kuma ya zama shugaban gwamnatin sojojin ƙasar.

Leave a Reply

%d bloggers like this: