Ƙasar Isra’ila ta amince a tsagaita wuta na awanni huɗu a kullum a arewacin Gaza, don a bai’wa fararen hula damar ficewa daga yankin.

Fadar gwamnatin Amurka ce ta sanar da hakan a yau Alhamis, duk da cewa shugaban ƙasar Joe Biden ya ce babu cikakkiyar tsagaita wuta.

Biden ya yabawa Fara-ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu bisa ɗan dogon hutu a faɗan, bayan tsawon wata daya da aka ɗauka ana fafata rikicin.

Sojojin Hamas da Isra’ila yanzu kowanne yana maɓoyarsa, kusa da inda ake gwabza faɗan a birnin Gaza, a yankin arewacin Zirin Gaza.

Mai magana da yawun sashin tsaron ƙasar  John Kirby ya sanar da manema labarai cewa, Isra’ila za ta fara Ƙaddamar da Dakatar da faɗan na awanni huɗu a kullum a yankin na Arewacin na Gaza.

“Isra’ilawa sun sanar da mu cewa, ba za a samu aikin sojin su a yankin ba na tsawon lokutan da aka ɗauka, kuma hakan zai fara daga yau.”

Leave a Reply

%d bloggers like this: