Shugaban ƙasar Madagaska Andry Rajoelina ya sake lashe zaɓe karo na biyu, duk da kuwa ƙauracewa yin zaɓen da ƴan tsagin masu hamayya suka yi a yankin kudu maso Gabashin ƙasar ta tsuburin Afirka.

Andry ya samu kaso 58.95 cikin 100 na ƙuri’un da aka kaɗa, wanda hukumar zaben ƙasar ta sanar a yau Asabar.

Ƴan takarkarun tsagin hamayya Siteny Randrianasoloniaiko da Marc Ravalomanana sun samu kashi 14.4 da kuma kashi 12. 1 kowannensu.

Ƴan takarkarun tsagin hamayya su goma sun yi kira ga magoya bayansu da su ƙauracewa yin zaɓen, duk da kuwa an sanya sunayensu a jikin takardar ƙuri’ar zaben da aka riga aka buga.

Hukumar zaɓen ta ce kaso 46 cikin 100 sun fito kaɗa ƙuri’a, amman ba a ga fuskar ko ɗaya daga cikin ƴan takarkarun hamayya 12 a wajen sanar da sakamakon zaɓen ba ranar da safiyar yau Asabar.

Ƴan siyasar tsagin hamayyar sun zargi shugaba Rajoelina da ƙoƙarin cigaba da mulki ta hanyar da bata dace ba, sun zargi shugaban da bai’wa kotuna da jami’an hukumar zaben cin hanci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: